An tabbatar: Saraki, Tambuwal da sauransu za su bar APC a mako mai zuwa

An tabbatar: Saraki, Tambuwal da sauransu za su bar APC a mako mai zuwa

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saaraki da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal sun kai ma ranakunsu na karshe a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ana sa ran za su koma PDP a mako mai zuwa.

Saraki da Tambuwal tare da wasu gwamnonin APC, wadanda suka hada da Ahmed bdulfatah na jihar Kwara, da Samuel Ortom na jihar Benue, za su sauya shekar a tare.

An tabbatar: Saraki, Tambuwal da sauransu za su bar APC a mako mai zuwa

An tabbatar: Saraki, Tambuwal da sauransu za su bar APC a mako mai zuwa

Gabannin wannan yunkuri, Saraki, Tambuwal da wasu gwamnonin APC sun gana da shugabannin PDP sannan taresuka je jana’izar mahaifiyar Abubakar Baraje, shugaban sabuwar PDP wadda ya jagoranci gwamnoni shida wajen sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2013, gabannin zaben 2015.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo

Uche Secondus, shugaban PDP na kasa, Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers da Baraje na daga cikin manyan shugabannin PDP da suka tarbi Saraki da tawagar sabuwar APC a ranar Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel