Kudin zaben 2019: PDP da Sanatoci sun ki amincewa da bukatar Buhari

Kudin zaben 2019: PDP da Sanatoci sun ki amincewa da bukatar Buhari

Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kokarin kawo cikas a zaben 2019.

Buhari, a wata wasika da ya akewa majalisar dokoki a ranar Talata, ya bukaci a tura N228.8bn na sabbin ayyukan da majalisar dokoki ta kara a kasafin kudin 2018, domin daukar nauyin zaben 2018.

Kudin gudanar da zabe zai kama N242.4bn. kudin ayyukan da aka kara a kasafin kudin 2018 baki daya N578.3bn.

Don haka, shugaban kasar na son a cire N228.8bn daga kudin, inda hakan ne nufin ayyuka da dama za su hadu da cikas wajen rashin kudin aiwatar da su.

Kudin zaben 2019: PDP da Sanatoci sun ki amincewa da bukatar Buhari

Kudin zaben 2019: PDP da Sanatoci sun ki amincewa da bukatar Buhari
Source: Depositphotos

Da suke sukar Buhari, babban jam’iyyar adawar kasar, PDP tayi zargin cewa shugaban kasar na son kawo cikas ga zaben 2019 saboda an fada masa cewa ba zai yi tazarce ba.

KU KARANTA KUMA: Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Cewa hakan ya sabama kundin tsarin mulki.Haka zalika wasu sanatoci sun nuna adawarsu ga hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel