Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo

Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo

Yan sanda sun harbe Bukola Adeoye, daya daga cikin muggan yan fashi da suke tsere daga hannun yan sandan SARS a jihar Ondo.

Adeoye wadda aka fi sani dAgbara ya mutu a lokacin da ake musayar wuta day an sanda a ranar Laraba, bayan sun je fashi a yankin Ore dake jihar Ondo.

Dan fashin na daga cikin muggan yan fashi da suka tsere a inda suke tsare yan makonni da suka shige.

Gbena Adeyanju, kwamishinan yan sandan jihar, ya tabbatar da mutuwar Adeoye yayinda yake gurfanar da gawarsa a gaban manema labarai a Akure.

Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo

Yan sanda sun harbe Agbara, daya daga cikin muggan yan fashi da ake nema ruwa a jallo
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa dan fashin a kama shi ne tare da wasu masu laifi bakwai sannan kuma ya kasance a shari’an fashi da makami a jihar.

KU KARANTA KUMA: Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Ya kara da cewa rundunar ta samu kira daga mambobin jama’a cewa yan fashi na aiwatar da fashi hankali nkwance a yankin Sabo Ore a tare da kalubale ba.

Ya bayyana cewa an kai mai laifin asibiti a take ainda ya mutu yan sa’o’i kadan bayan an kwantar da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel