Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli ya nemi doki kan sintirin da helikoftan yan sanda ke yi a gidan gwamnati.

Fayose yace helikoftan yan sandan na nufin barazana ga rayuwarsa, iyalansa, ma’aikata dab akin dake zwa gidan gwamnati.

Ya nuna rashin amincewa da sintirin da helikoftan ke yi a gidansa da ofishinsa duk da cewar an kammala zaben gwamna a jihar tun a ranar 14 ga watan Yuli.

A wata sanarwa daga babban mai kakakinsa, Idowu Adelusi, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin “cin zarafin mulki daga gwamnatin tarayya.”

Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Helikoftan Yan sanda na barazana a rayuwa na – Fayose

Ya kuma zargi hukumomin tsaron kasar da bari ana amfani da su wajen barazana ga abokan adawan siyasa duk da cewar ana biyansu da kudin masu biyan haraji.

KU KARANTA KUMA: Manoma ga naku: Yadda zaka kaucewa sayan jabun magani a kasuwani

A cewarsa ya zama dole hukumoin tsaro su guje ma siyasa sannan kada su mayar da kansu Karen farautan yan siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel