Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin Buhari

- Har yanzu dai Obasanjo bai kyale gwamnatin Buhari ba

- Tsohon shugaban kasar ya sake sukar salon yadda Buhari ke tafiyar da mulkinsa

- A cewar Obasanjon, Buhari ya sakarwa wasu ragamar gudanar da mulkin kasar nan

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sake sukar gwamnatin tarayyar kasar nan, inda ya bayyana shugaba Muhammad Buhari a matsayin wanda ya kasa tabuka komai akan mulki, wanda sakacinsa ya sanya ake samun zubar da jini ta hanyar kashe-kashe da kuma kangin talauci a kasar nan.

Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Buharin ta shiga rudani tare da jefa ‘yan kasar nan wani halin ha'ula'i.

Sannan ya kara da cewa a maimakon shugaban kasar ya mayar da hankali wajen fitar da kasar daga cikin halin da tsinci kanta, amma sai ya bige da mika gabarin kasar ga wasu mutane.

KU KARANTA: Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata

Obasanjo ya bayyana hakan ne ta bakin tsohon gwamnan jihar Osun Prince Olagunsoye Oyilola a gurin wani taro na kwana daya da manyan kungiyoyin Afenifere da Ohanaeze Ndigbo da kuma kungiyar kare ‘yankin Neja Delta tare da kungiyar dattawan arewacin kasar nan.

Idan za'ai iya tunawa dai tsohon shugaban kasar ya dade yana sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari akan yadda ta ke tafiyar da mulki a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel