Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu

Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu

Idan ba a mance ba kwanakin baya majiyarmu Legit.ng ta taba kawo muku labarin wasu 'yan fashi da rundunar 'yan sandan SARS ta kama a jihar Ondo

Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu

Wasu 'yan fashi sun asirce jami'an 'yan sanda sun gudu
Source: Depositphotos

Wasu 'yan fashi da makami da ake zargi, Bukola Adeoye da Rotimi Adeyeye, wadanda suka samu nasarar arcewa daga hannun rundunar 'yan sandan SARS reshen garin Akure, babban birnin jihar Ondo, ana zargin sun yiwa jami'an 'yan sandan dake kan aiki a lokacin asiri ne suka samu suka gudu.

Idan ba a mance ba kwanakin baya majiyarmu Legit.ng ta taba kawo muku labarin wasu 'yan fashi da rundunar 'yan sandan SARS ta kama a jihar Ondo, wadanda suka gudu daga hannun jami'an 'yan sandan.

DUBA WANNAN: Maduro: Afirka ce ta lashe wasan kwallon kafa na duniya da aka buga a Rasha

Budurwar wani daga cikin wadanda ake zargin mai suna, Loveth Ogbu, wacce jami'an 'yan sandan suka kama, ta bayyana manema labarai a ranar Larabar nan, cewar bata taba sanin cewa saurayin nata dan fashi bane.

An kama Ogbu tare da wasu 'yan fashin guda biyar wadanda ake zargin suma suna kungiya daya ne dasu Adeyeye da Adeoye.

Ogbu, wacce take aikin sayar da giya, tace tana zaune da Adeyeye a garin Akure, ta ce a lokacin data tambayeshi wane irin aiki yake yi, sai yace tayi shiru kada ta fadawa kowa ko kuma ya kasheta.

Ta ce, "Ni budurwar Rotimi Adeyeye ce, muna zaune dashi a unguwar Ijoka dake garin Akure. Ban san cewa shi dan fashi bane har sai da 'yan sanda suka kama shi. 'Yan sandan sun sanar dani cewa shi da abokin shi Bukola Adeoye 'yan fashi ne.

"A lokacin da suke hannun 'yan sandan, dan uwansa mai suna Barrister, ya basu wata laya wacce ya ce suyi amfani da ita ga jami'an 'yan sandan su gudu. Kuma shine ya taimaka ya kunce su bayan sun gudu daga wurin 'yan sandan."

Bayan haka, Kwamishinan 'yan sanda na jihar Mr. Gbenga Adeyanju, yace bayan Adeyeye da Adeoye sun gudu daga hannun jami'an 'yan sandan, sun gudu garin Ore dake karamar hukumar Odigbo a jihar Ondo, inda suka cigaba da aikata fashin su.

Sannan ya bayyana cewar budurwar Adeyeye, Ogbu ita ce ta taimaka musu suka san inda suke boyewa. Kwamishinan yace bayan sunje wurin da suke sunyi artabu dasu kafin suka samu suka harbi Adeoye, inda shi kuma Adeyeye ya sake guduwa. Daga baya Adeoye ya mutu a asibiti sanadiyyar ciwon da yaji a lokacin kamo shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel