Wasu ‘yan fashi sunyiwa jami’an SARS asiri sun tsere bayan kama su

Wasu ‘yan fashi sunyiwa jami’an SARS asiri sun tsere bayan kama su

- Tsafi gaskiyar mai shi, 'yan fashi sunyi amfani da asiri sun sulale

- Ana zargin wani lauya ne ya kai musu wasu layoyi yayinda suke tsare

- Sai dai kuma bayan tserewarsun jam'ian sun sake binsu don nemo su

Mutum biyun da ake zargin yan fashi da makami ne masu suna Bukola Adeoye da Rotimi Adeyeye, sun tsere daga hannun jami'an rundunar ‘yan sandan SARS na reshen jihar ondo, ta hanyar amfani da wani sihiri.

Wasu ‘yan fashi sunyiwa jami’an SARS asiri sun tsere bayan kama su

Wasu ‘yan fashi sunyiwa jami’an SARS asiri sun tsere bayan kama su

Tun da farko rahotanni sun bayyana cewa an tsare su ne bisa zargin fashi da makami da su kayi a garin Akure a wasu makwanni da suka gabata, kwatsam sai gashi sun tsere daga hannun jami'an ‘yan sandan duk da cewa an sanya musu ankwa.

Jim kadan da cafke ‘yan fashin, sai jami'an rundunar ‘yan sandan su ka damke budurwar daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Loveth Ogbu mai sana'ar sayar da giya tare da gabatar da ita da sauran wasu ‘yan fashi da makami guda 5, domin zurfafa bincike.

"Ni budurwar Rotimi ce, mun dade da shi tare, muna zaune da shi ne a yankin Ikoja da ke birnin Akure, amma ni ban san sana'arsa fashi da makami ce ba, domin na taba tambayarsa sana'arsa inda ya yi min barazanar kashe ni" in ji Loveth.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun harbe wata mata yayin zanga-zangar da suke yi kan kashe abokan aikinsu 2 a Kaduna

Ta kara da cewa sai bayan da ya fada komar jami'an tsaro ne, take samun labarin cewa saurayi nata dan fashi da makami ne.

Ta kuma bayyana cewa a lokacin da suke tsare a hannun yan sanda ne, wani babban yayansu wanda kuma lauya ne, shi ne ya basu wani abu na siddabaru da su ka yi amfani da shi suka tsere.

A nasa bangaren kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ondo Mista Gbenga Adeyanju, ya bayyana cewa yan fashin da suka tsere daga hannun ‘yan sandan SARS din sun koma kauyen Ore dake karamar hukumar Odigbo ta jihar Ogun, inda suka cigaba da aikata laifuffuka.

"Mun yi amfani da budurwar daya daga cikinsu wajen ganin mun cafke su, inda jami'an mu suka je maboyarsu, bayan musayar wuta da aka yi da yan fashin wanda hakan ya jikkata daya daga cikinsu, inda aka garzaya da shi asibiti domin ceton rayuwarsa sai dai a can ne rai yayi halinsa, amma mun yi nasarar damke abokin fashin nasa" in ji kwamishinan yan sanda Gbenga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel