‘Yan Majalisar dokokin Ekiti na shirin tafiya dogon hutu bayan sun soki zaben Gwamna da aka yi

‘Yan Majalisar dokokin Ekiti na shirin tafiya dogon hutu bayan sun soki zaben Gwamna da aka yi

Ba da dadewa bane mu ke jin cewa wani rikici ya nemi ya kaure a Majalisar dokokin Jihar Ekiti inda ‘Yan Majalisar PDP wadanda su ke da rinjaye su ka nemi a dage zaman Majalisar sai Oktoba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘Yan Majalisar Jihar Ekiti sun shiga takaddama sa’ilin da aka nemi a tafi wani dogon hutun kusan watanni 3. Majalisar sun kuma yi tir da zaben da aka yi a makon jiya wanda Kayode Fayemi yayi nasara.

‘Yan Majalisar sun dage zaman har sai nan da Watan Okotoba ne saboda barazanar da Jami’an tsaro su kayi masu. Sai dai wasu ‘Yan Majalisan da ke karkashin Jam’iyyar APC sun nuna matukar rashin amincewan su game da wannan matakin.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Jami’an ‘Yan Sanda ne su ka garkame mutane na – Fayose

Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Cif Gboyega Aribisogan da wasu ‘Yan APC sun bayyana cewa shugabannin Majalisar sun dauki wannan mataki ne domin amsawa bukatun Gwamna Ayo Fayose wanda ke shirin barin kujerar sa kwanan nan.

Sauran ‘Yan Majalisar da ke karkashin APC irin su Sunday Akinniyi da Adeniran Alagbada sun ce dage zaman bai dace ba, kuma cin amanar wadanda su ke wakilta ne. Su dai ‘Yan PDP masu rinjaye sun ce Jami’an tsaro ne ke neman ganin bayan su.

Kun san cewa ‘Dan takarar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi ya doke Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan da aka yi. Gwamna Ayo Fayose ya sha kunya a zaben da aka yi a karshen makon jiya inda yayi kukan an tafka magudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel