Jama’a sun ce Gwamnatin Buhari ta cancanci yabo na dawo da jirgin Nigerian Airways

Jama’a sun ce Gwamnatin Buhari ta cancanci yabo na dawo da jirgin Nigerian Airways

Jama’a da dama sun yaba da kokarin da da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi na dawo da kamfanin jirgin saman Najeriya bayan shekaru akalla 15 da Gwamnatin PDP ta kashe kamfanin jirgi na kasar.

Ministan sufurin jiragen saman Najeriya Hadi Sirika

A jiya ne aka kaddamar da tambari da samfurin jirgin saman na Najeriya da za ayi aiki da su a shekara mai zuwa. Wani Bawan Allah mai suna A. Ayekaooto ya yabi Shugaba Buhari inda yace cigaban kasa ya sa gaba.

A lokacin da wasu manya su ka maida hankali wajen ganin masu kudi sun mallaki jirage, Shugaba Buhari yayi kokari ne na dawo da kamfanin jirgin kasar mai suna Nigeria Airways da ake sa rai zai fara aiki shekaran badi.

KU KARANTA: Majalisa na wani sabon bincike kan Ministan man fetur

Gwamnati tace ba za ta shiga cikin harkar tafiyar da jiragen ba domin za a saki komai ne ga ‘Yan kasuwa. Dalilin haka ne wani Bawan Allah Jibril Gawat yayi Allah wadai da masu sukar lamarin Gwamnatin Tarayyar ko ta ina.

Jama’a da dama dai sun sa albarkacin bakin su inda wani mai suna Yinka Ogunnubi ta shafin sa na Tuwita yayi addu’ar hakar Gwamnatin ta cin ma ruwa. Mutane dai sun yaba da irin kokarin da Ministan kasar Sanata Hadi Sirika yayi.

Jiya kun ji labari cewa an kammala yashe kogin Neja, jiragen ruwa zasu fara shigowa Arewacin Najeriya cikin sauki. Shugaban hanyoyin ruwan cikin gidan kasar nan ya bayyana wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel