Mutane kusan 500 sun tsere daga PDP sun dawo APC a Kuje

Mutane kusan 500 sun tsere daga PDP sun dawo APC a Kuje

- Wasu manyan PDP sun dawo tafiyar Jam’iyyar APC a Garin Abuja

- Tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar sun sha alwashin kada PDP yanzu a 2019

Labari ya zo mana jiya cewa an samu wasu daruruwan mutane da su ka fice daga Jam’iyyar PDP a Abuja. Jam’iyyar APC dai tayi wani babban kamu ne a Yankin Kuje da ke cikin Babban Birnin Tarayya watau Abuja.

Mutane kusan 500 sun tsere daga PDP sun dawo APC a Kuje

Wasu manuyan PDP sun fice daga Jam'iyyar sun koma APC

Sahara Reporters ta rahoto cewa wasu manyan jiga-jigan PDP da ke Kuje da ke cikin Garin Abuja sun sauya sheka sun dawo Jam’iyyar APC inda su ka koka da kama-karyar da ake yi a Jam’iyyar adawan kasar na PDP.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin APC a Arewa da kafar su guda ta bar Jam’iyyar

Yahaya Mohammed Gambo wanda shi yayi jawabi a madadin sauran mutum500 da su ka fice daga Jam’iyyar PDP yace za su yi bakin kokarin su na ganin sun tika PDP da kasa a zabe mai zuwa da za ayi a shekarar 2019.

Sauran wadanda su ka bar Jam’iyyar PDP sun hada da jiga-jigan ta a Yankin irin su Sarkin Samarin Kayarda, Alhaji Idris Sabo, Ramatu Idris, da sauran su. Shugaban APC na Kuje Godwin Poyi ne ya karbe su yayi masu wanka.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kishin-kishin din su Bukola Saraki da wasu manyan Gwamnonin APC irin su Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom za su koma PDP kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel