Gwamna El-Rufai ya fara shirin 2019, ya nada sabbin Sojojin yakin neman zabe

Gwamna El-Rufai ya fara shirin 2019, ya nada sabbin Sojojin yakin neman zabe

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, yan siyasa a matakai daban daban sun fara shirin tunkarar zaben tare da shirin ko ta kwana, inda anan ma aka ruwaito gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kaddamar da nasa shirin.

Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya nada wasu hadimansa na kusa wasu muhimman mukamai a tafiyar yakin neman al’ummar jihar Kaduna su sake zabensa a matsayin gwamnan jihar Kaduna, karo na biyu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi ma Yansandan kwantauna bauna, guda ya rigamu gidan gaskiya

2019: Gwamna El-Rufai ya fara shirin yaki, ya nada sabbin Sojojin yakin neman zabe

El-Rufai da Buhari
Source: Facebook

Daga cikin wadanda suka samu wannan tagomashin jagorantar yakin neman zaben na El-Rufai akwai Malam Samuel Aruwan, Maryam Abubakar, Uba Sani, Hafiz Bayero, Muhammad Sani Dattijo da Muyiwa Adekeye.

El-Rufai ya nada kwamishinana tsare tsare Muhammad Sani Dattijo a matsayin Daraktan tsare tsare da bincike na yakin neman zabensa, Samuel Aruwan a matsayin Daraktan watsa labaru, sai Maryam Abubakar a matsayin Daraktan kula da kafafen sadarwa na zamani.

Sauran mukaman sun hada da Daraktan harhada kan yan siyasa, Malam Uba Sani, Daraktan hada kan matasa, Hafiz Bayero, sai kuma Daraktan tsare tsaren sadarwa, Muyiwa Adekeye.

Haka zalika gwamnan ya daura musu dawainiyar jagorantar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel