Babbar magana: Kaakakin jam’iyyar APC ya yi fatali da jam’iyyar, ya yi murabus

Babbar magana: Kaakakin jam’iyyar APC ya yi fatali da jam’iyyar, ya yi murabus

Kaakakin jam’iyyar APC reshen jihar Benuwe, Samuel Agbo ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda, inda a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli ya yi murabus daga mukaminsa, tare da ficewa daga jam’iyyar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Samuel ya danganta dalilinsa na ficewa daga APC ga gazawar jam’iyyar wajen biyan bukatun al’ummar jihar Benuwe, da nuna halin ko in kula da mawuyacin halin da jam’an jihar ke ciki, musamman matsalar tsaro da ta addabi jihar.

KU KARANTA: Barka: An kammala yashe kogin Neja, jiragen ruwa zasu fara shigowa Arewacin Najeriya

“APC ta gagara yi ma jihar Benuwe adalci, duba da rikon sakainar kashi da gwamnatin tarraya ke yi ma matsalolin tsaro da suka fitini jihar a cikin yan shekarun nan, uwar jam’iyyar APC a jihar Benuwe ta yi min tayin alkawurra da dama akan kada na fita, amma ba zan iya sadaukar da rayuwan dubunan jama’a ba saboda wabi abin duniya.” Inji shi.

Samuel ya kara da cewa take taken shugaba Buhari da wasu manyan jami’an gwamnatinsa sun nuna basu da nufin kawo karshen kashe kashe a jihar Benuwe, amma kuma ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan jihar Benuwe ta bangare gudanar da kyakkyawan shugabanci.

Idan za’a tuna a ranar Litinin,16 ga watan Yuli ne gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda yace a yanzu haka yana laluben jam’iyyar da ta fi dacewa da shi, shima tsohon Kaakakin APC yace zai bi Gwamnan zuwa duk jam’iyyar daya fada.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel