Yan bindiga sun yi ma Yansandan kwantauna bauna, guda ya rigamu gidan gaskiya

Yan bindiga sun yi ma Yansandan kwantauna bauna, guda ya rigamu gidan gaskiya

Wani jami’in Dansanda ya gamu da ajalinsa a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli a yayin da wasu gungun yan bindiga suka bindige shi har lahira a daidai hanyar Akwanga zuwa Wamba, a jihar Nassarawa, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Samaila Usman ne ya tabbatar da haka a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli, a yayin wata ganawa da yayi da manema labaru a garin Lafia.

KU KARANTA: Barka: An kammala yashe kogin Neja, jiragen ruwa zasu fara shigowa Arewacin Najeriya

“A ranar 15 ga watan Yuli ne wasu Yansanda dake aikin sintiri suka fada tarkon kwantan bauna da wasu gungun yan fashi da makami suka shirya ta hanyar sanya shinge akan hanya, anan aka shiga musayar wuta, inda aka wani Dansanda ya samu rauni, kuma ya rasu bayan an garzaya da shi Asibiti.

“Hakazalika Yansanda sun kashe mutum daya daga cikin yan fashin, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi daban daban a jikkunansu, duk da haka Yansanda na farautarsu ruwa a jallo a yanzu haka.” Inji shi.

Daga karshe, Kaakaki Usman ya bayyana cewa sun kwato bindiga kirar AK 47 daga wajen yan bindigan, tare da dimbin alburusai da makamai da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel