An kama wasu mutane 7 masu hannu a rikicin jihar Filato

An kama wasu mutane 7 masu hannu a rikicin jihar Filato

- Jami'an tsaro na cigaba da samun nasarar cafke wadanda ke tada zaune tsaye a Filato

- Wannan karonma Sojoji sun sake damke wasu mutane da ake zargin suna da hannu dumu-dumu a ciki

Jami'an rundunar sojin kasar nan sun sake samun nasarar damke wasu mutane guda bakwai masu alaka da rikicin da ya faru a jihar Filato.

An kama wasu mutane 7 masu hannu a rikicin Jihar Filato

An kama wasu mutane 7 masu hannu a rikicin Jihar Filato

Babban daraktan yada labarai na ma'aikatar tsaro ta kasa John Agim ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Talata a birnin Jos.

Ya bayyana cewa jami'an sojoji na cigaba da kokari wajen binciko masu hannu a rikicin da ya faru a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata, wanda kawo yanzu suka samu nasarar cafke mutane guda bakwai.

KU KARANTA: Makiyaya sun damke barayin shanayensu yayinda suka kawo kasuwa sayarwa, sun kashe su nan take

Wadanda aka damke din dai sun hada da Ibrahim Joji da kuma Madu Ibrahim, sauran su hada da Shuaibu Suleiman da Zakamin Abdulkadir. Ya kara da cewa wadannan mutanen suna da hannun a rikice-rikice da akayi ta fama da wasu a watan Yunin, Musamman a yankin kananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi.

A karshe Babban daraktan ya ce wadanda ake zargin ba'a same su da wani makami ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel