Saraki, Secondus, Wike sun halarci addu’an mutuwar Aisha Baraje

Saraki, Secondus, Wike sun halarci addu’an mutuwar Aisha Baraje

Shugabannin Najeriya daga jam’iyyun kasar daban-daban sun halarci jana’izar mahaifiyar marigayiya Alhaja Aishat Baraje, mahaifiyar Alhaji Abubakar Baraje, baabban jigon kungiyar sabuwar APC kuma abokin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Daga bisani shugabannin sun yi ganawa a gidan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Saraki, Secondus, Wike sun halarci addu’an mutuwar Aisha Baraje

Saraki, Secondus, Wike sun halarci addu’an mutuwar Aisha Baraje

Wadanda suka halarci jana’izan sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus, gwwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmad, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Dr Sule Lamido, Sanata Barnabas Gemade, Abubakar Baraje da sauran yan siyasa.

KU KARANTA KUMA: Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokoki, Shehu Sani ya bayyana cewa girman kai zai kai fadar shugaban kasa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ya baro a zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja. Ya bayyana cewa tuni fadar shugaban kasa ta rufe duk kofofi ga masu yiwa jam’iyyar biyayya da son ganin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu nasara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel