Girman kai zai kai APC ya baro – Shehu Sani

Girman kai zai kai APC ya baro – Shehu Sani

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokoki, Shehu Sani ya bayyana cewa girman kai zai kai fadar shugaban kasa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ya baro a zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja. Ya bayyana cewa tuni fadar shugaban kasa ta rufe duk kofofi ga masu yiwa jam’iyyar biyayya da son ganin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu nasara.

Girman kai zai kai APC ya baro – Shehu Sani

Girman kai zai kai APC ya baro – Shehu Sani

Ya kara da cewa sai yan Najeriya sun tsaya tsayin daka sannan gwamnati mai mulki zata dauki mataki akan kalubalen da kasar ke fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

Ya jadadda cewa shugaba Buhari kadai ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba, kuma ya kamata ya yadda da haka sannan kuma jam’iyya mai mulki ma ta fahimci haka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel