Abinda gwamnatin tarayya zata yi domin magance yawaitar kashe-kashe - IBB

Abinda gwamnatin tarayya zata yi domin magance yawaitar kashe-kashe - IBB

- Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya shawarci gwamnatoci matakai daban-daban da su zama masu kokarin kiyaye afkuwar barkewar rikici

- A wata takardar jaje da ya aike ga mutanen da ambaliyar ruwa harin ta'addanci ya shafa, IBB ya bukaci shugabannin al'umma su hada kai da gwamnati domin kawo karshen matsalolin tsaro

- IBB ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga jama'ar jihohin Katsina da Sokoto da kuma bisa asarar rayukan 'yan uwansu sanadiyar ambaliyar ruwa da harin 'yan bindiga

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya shawarci gwamnatoci matakai daban-daban da su zama masu kokarin kiyaye afkuwar barkewar rikici domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar su.

A wata takardar jaje da ya aike ga mutanen da ambaliyar ruwa harin ta'addanci ya shafa, IBB ya bukaci shugabannin al'umma su hada kai da gwamnati domin kawo karshen matsalolin tsaro a kasar nan.

Abinda gwamnatin tarayya zata yi domin magance yawaitar kashe-kashe - IBB

Ibrahim Badamasi Babangida

Kazalika tsohon shugaban kasar ya nuna damuwarsa bisa yawaitar kai hare-hare kan jami'an tsaro yana bayyana hakan a matsayin abun takaici.

DUBA WANNAN: Bayan kammala zaben Ekiti, Obasanjo ya sake rubuta wata sabuwar wasikar

IBB ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga jama'ar jihohin Katsina da Sokoto da kuma bisa asarar rayukan 'yan uwansu sanadiyar ambaliyar ruwa da harin 'yan bindiga.

"Akwai annoba wacce babu wanda zai iya hana afkuwar ta, amma idan gwamnati zata kasance mai kiyaye wa, za a samu saukin aiyukan ta'addanci," a cewar IBB.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel