Ortom ba zai bar APC ba – Wambai

Ortom ba zai bar APC ba – Wambai

Mataimakin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Arewa maso tsakiya Alhaji Suleiman Wambai, ya bayyana cewa gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ba zai bar jam’iyyar ba.

Wambai wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba da yake hira da manema labarai ya bayyana cewa gwamnan bai rubuta wasika ga jam’iyyar game da batun sauya shekarsa ba, inda ya ce duk da rashin ji daga gwamnan, hedkwatar jam’iyyar ta dauki mataki don sanya baki a lamarin.

“Mun ga rahotanni dama a gidajen watsa labaru daban-daban cewa gwamnan yace an bashi takardan sallama, don haka mun dauki matakai.

Ortom ba zai bar APC ba – Wambai

Ortom ba zai bar APC ba – Wambai

“Shugabanmu ya rigada ya gayyaci gwamnan da sauran jam’iyyu masu ra’ayi daga jihar Benue domin magance lamarin.” Inji shi.

KU KARANTA KUMA: Tsare-tsarenka na iya kawo sauyi a Najeriya – IBB ga Turaki

Ya bayyana cewa jam’iyyar APC karkashin jagorancin sa zata yi duk kokarin don ganin xewa sun zaben zabe a dukkanin yankuna kasaer a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel