Da sake: Kungiyoyin kasar waje sun ce akwai gyara a zaben Ekiti

Da sake: Kungiyoyin kasar waje sun ce akwai gyara a zaben Ekiti

Dazu mu ka ji labari cewa wasu Kungiyoyin kasar waje da su ka halarci zaben Gwamnan Jihar Ekiti da aka yi kwanan nan sun ce akwai gyara a zaben don kuwa bai cika sharudan da su ka dace ba.

Da sake: Kungiyoyin kasar waje sun ce akwai gyara a zaben Ekiti

Ana zargin an yi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben Ekiti

Kungiyoyin da su ka zura idanu lokacin zaben sabon Gwamnan Ekiti sun tabbatar da cewa akwai nakasa a zaben. A baya dai Gwamna Ayo Fayose ya zargi Jami’an tsaro da tafka magudi domin ganin Jam’iyyar APC tayi nasara.

Punch ta rahoto cewa Kungiyoyin kasar waje da na gida da aka yi zaben a gaban su sun bayyana cewa tabbas akwai nakasa a zaben na kwanan nan. Masu sa-ido game da zaben sun hada da mutane da aka dauko daga Kasashen Duniya.

KU KARANTA: Wani Jigo a siyasar Najeriya ya nemi PDP ta kwantar da hankalin ta

Kungiyoyin Duniya da masu kare hakkin Bil Adama fiye da 50 sun yi ittifaki cewa an samu matsala a zaben musamman daga wajen Jami’an tsaro. An dai yabawa Hukumar zabe na INEC, amma an soki Jami’an tsaron kasar.

An dai aika ‘Yan Sanda 30, 000 ne zuwa zaben wanda Kungiyoyin su kace bai dace ba. An kuma koka da yadda aka rika sayen kuri’u kuru-kuru a gaban Jama’a a wajen zaben. An dai kuma yabawa na’urorin zaben da aka yi amfani da su.

Zargin rashin adalcin da aka yi a zaben ne yasa Gwamnan na Ekiti mai shirin barin kujera watau Ayo Fayose ya tashi ya sanar da sakamakon zabe a gidan rediyo inda ya bayyana cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel