Majalisar Wakilai ta bukaci Sufeto Janar ya lalubo makasan jami'an 'yan sanda 4 a jihar Edo

Majalisar Wakilai ta bukaci Sufeto Janar ya lalubo makasan jami'an 'yan sanda 4 a jihar Edo

Majalisar wakilai ta bukaci sufeto janar na 'yan sanda Ibrahim K. Idris, akan ya gaggauta kafa wani kwamitin jami'an bincike domin bankado wadanda ke da hannu cikin ta'addancin kisan wasu jami'an 'yan sanda hudu a jihar Edo.

Rahotanni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne aka yiwa wasu jami'an yan sanda hudu kisan gilla yayin da suke bakin aiki akan hanyar Sabongida-Ora dake karamar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo.

Legit.ng ta samu rahoton cewa baya ga kashe jami'an, 'yan ta'addan sun kuma sanya gawar su cikin motar su ta aiki kana suka banka ma ta wuta kuma suka kama gaban su.

Mataimakin shugaba mai rinjaye na majalisar, Mista Pally Iriase, shine ya kawo wannan batu a farfajiyar majalisar yayin gudanar da zamanta a ranar yau ta Laraba cikin muhimman ababe da suka shafi al'umma dake bukatar kulawa ta gaggawa.

Majalisar Wakilai ta bukaci Sufeto Janar ya lalubo makasan jami'an 'yan sanda 4 a jihar Edo

Majalisar Wakilai ta bukaci Sufeto Janar ya lalubo makasan jami'an 'yan sanda 4 a jihar Edo

Cikin jawaban sa, Pally ya hikaito yadda aka zartar da wannan mummunan ta'addanci kan jami'an wanda kawowa yanzu ba bu amo ballantana labari dangane da wadanda suka aikata shi.

Yake cewa, wannan lamari na kai hare-hare kan jami'an 'yan sanda ya fara zama ruwan dare kasar nan cikin wannan lokuta da ya kamata gwamnati ta mike tsaye wurjanjan domin daukar mataki.

KARANTA KUMA: 'Yan Fashi da Makami sun kar wani Jami'in dan sanda har Lahira a jihar Nasarawa

A yayin haka kuma shugaba mai rinjaye na majalisar Mista Yakubu Barde ya bayyana cewa, an yiwa wasu jami'an 'yan sanda biyu makamanciyar wannan kisan gilla kan hanyar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar Talatar da ta gabata.

Majalisar yayin zaman nata ta yanke shawara ta neman Sufeto Janar ya kafa wani kwamitin jami'ai na musamman domin damko wadanda ke da hannu cikin wannan mummunan laifi da zai janyowa kasar nan zagon kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel