An yankewa wata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza

An yankewa wata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza

A yau Laraba, wata kotun majistare dake Ile-Ife a jihar Osun ta yanke wa wata mata, Damilola Toromade, hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku saboda ta yiwa wata matan aure jina-jina da reza a wuya.

Alkalin kotun, Mrs. A.A. Olowolagba ta zartar da hukuncin a kan Toromade mai shekaru 26 bayan ta amsa laifinta.

Olowolagba tace abin takaici da bakin ciki ne yadda matashiyar budurwa kamar Toromade zata iya jiwa yar uwarta mace irin wannan mummunan raunin.

An yankewa wata mata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza

An yankewa wata mata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza

DUBA WANNAN: Assha: 'Yan bindiga sun sake yin mummunan ta'addi a wata kauye a Zamfara

Tace kamata ya yi wanda ake yanke wa hukuncin tayi amfani da lokacin ta da karfinta wajen gudanar da ayyukan da zasu amfane ta a maimakon cin zarafin mutane.

"Abinda ya dace da mutane masu irin halinki shine a kulle ku har lokacin da kuka sauya halayen ku.

"Saboda laifin da kika aikata, an zartar miki da hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku ba tare da zabin biyar tara ba," inji Alkaliyar.

Olowolagba tace tana fatan wannan hukuncin data zartas zai sama izina ga wasu masu ra'ayin aikata barna mai kama da wadda Toromade ta aikata.

Da fari, Dan sanda mai shigar da kara, Inspecta Sunday Osanyintuyi, ya shaidawa kotu cewa wadda ake tuhumar da aikata laifin ne ranar 15 ga watan Yuli misalin karfe 10.40 na safiya a Kwallejin Oduduwa dake Ile-Ife.

Osanyintuyi yace wanda ake tuhumar ta doki wata Kudirat Adefamo kuma tayi amfani da reza tayi mata rauni.

Laifin ya sabawa sashi na 335 na dokar masu laifi na jihar Osun 2002.

Wanda aka yanke wa hukuncin ta roki kotu tayi mata rangwame kasancewa bata da lauya mai kare ta kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel