Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wasu mambobin majalisar dokokin kasar dake kungiyar sabuwar APC (R-APC) na iya barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) s a ko wani lokaci.

Wata majiya dake sane da abubuwan dake faruwa a jam’iyyar APC ta fadama jaridar New Telegraph cewa shugaban majalisar dattawan da wasu yan majalisa za su bar APC kafin majalisar dokokin kasar ta tafi hutun shekara a mako mai zuwa.

Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

Saraki da yan majalisa sun gama tsare-tsaren barin APC - Majiya

Jaridar ta ruwaito cewa Saraki na ta tattaunawa da shugabannin APC a matakan kasa da na jihar Kwara gabannin barinsa jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yara yan arewa miliyan 12 basa makaranta – Inji Ango Abdullahi

An tattaro cewa shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Litinin, 16 ga watan Yuli ya ziyarci Saraki a gidansa sannan ya bukaci da kada shugaban majalisar dattawan ya bar jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel