Gwamnonin APC 2 da ake rade-radin zasu bar jam'iyyar sun yi taro da PDP

Gwamnonin APC 2 da ake rade-radin zasu bar jam'iyyar sun yi taro da PDP

Gwamna jihar Sakkwato kuma tsohon Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Aminu Waziri Tambuwal tare da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed sun gana da shugabanin jam'iyyar PDP don tattaunawa kan wasu abubuwa a yau Laraba.

Rahottani da wasu masu nazarin harkokin siyasa ke yadawa shine gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC suna shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP ne.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnonin biyu tare da takwaransu na jihar Benue Samuel Ortom suna shirin ficewa daga jam'iyyar ta APC.

Gwamnonin APC 2 da ake rade-radin zasu bar jam'iyyar sun yi taro da PDP

Gwamnonin APC 2 da ake rade-radin zasu bar jam'iyyar sun yi taro da PDP

DUBA WANNAN: Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

A ranar Litini data gabata, gwamna Ortom ya snaar da cewa jam'iyyar APC ta bashi 'jan kati' kuma hakan na nufin yana iya komawa duk jam'iyyar da yake ra'ayyi.

Gwaman Rivers, Nyesom Wike yana daya daga cikin wadanda suka hallarci taron da aka kammala mintuna 15 da suka wuce.

Tabuwal da Ahmed da Ortom suna daga cikin mambobin sabuwar PDP wanda suka shigo cikin jam'iyyar APC domin kawar da PDP daga mulki a shekarar 2015.

Watanni uku da suka wuce, shugabanin nPDP sun zargi uwar jam'iyyar da mayar dasu saniyar ware. Sun kuma bukaci a basu damar ganawa da shugaba Muhammadu Buhari amma yaki amincewa ya gana dasu, sai dai ya bukaci su gana da mataimakinsa Osinbajo.

Ku biyo mu don samun karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel