Wani 'Dan shekara 52 ya zakkewa wani Matashi mai shekara 14 ta Dubura a jihar Legas

Wani 'Dan shekara 52 ya zakkewa wani Matashi mai shekara 14 ta Dubura a jihar Legas

A ranar Larabar da ta gabata ne wani dattijo dan shekara 52, Emeka Nwobochi, ya yanki tikitin baiwa diga-digan sa hutu a gidan kaso na Kirikiri yayin da wata kotun majistire ta zarge shi da aikata alfasha da wani matashi mai shekaru 14 a jihar Legas.

Alkaliyar kotun Misis B. O Osunsanmi, ta yi kunnen uwar shegu kan roko da begen wannan dattijo, inda ta garkame shi a gidan kaso domin samun dama ta nemi shawarar babbar cibiyar zartar da hukunci ta jihar.

Kamar yadda ASP Ezekiel Ayorinde ya bayyana, jami'in dan sanda mai shigar da korafi a gaban kotu ya bayar da sheda da cewar Mista Emeka ya aikata wannan mummunan laifi ne a ranar 29 ga watan Yuni a tashar Mota ta Maza Maza dake jihar ta Legas.

Wani 'Dan shekara 52 ya zakkewa wani Matashi mai shekara 14 ta Dubura a jihar Legas

Wani 'Dan shekara 52 ya zakkewa wani Matashi mai shekara 14 ta Dubura a jihar Legas

Rahotanni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wannan dattijo ya zakkewa Matashin ne ta dubura inda ya gaza jure radadin wannan keta haddi da ya sanya ya shigar da korafin damuwar sa ba tare da wata-wata ba.

KARANTA KUMA: Kotu ta jefa wani Matashi gidan wakafi bisa laifin satar N6, 500 da wayar Salula

Lamarin dai ya afku ne yayin da wannan Dattijo ya dauko matashin daga kauyen su a can jihar Abia da manufar sanya a makaranta bayan rasuwar Mahaifin sa da kuma rashin kula daga bangaren Mahaifiyar sa yayin da tayi sabon aure.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan laifi ya sabawa sashe 261 cikin dokokin jihar Legas wanda babu wani hukunci face na daurin rai-da-rai ga wadanda suka aikata.

A halin yanzu dai kotun ta daga sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Agusta domin zartar da hukuncin wannan mummunan laifi mai ban kyama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel