Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi

Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar da takardan shaidardawowa mulki ga Dr Kayode Fayemi, wanda ya lashe zaben jihar Ekiti.

Kwamishinan huumar INEC na kasa, Mista Solomon Soyebi ya gabaar da takardan ga gwamnan mai jiran gado a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli a hedkwatar hukumar dake Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Dr Fayemi, mai shekaru 53 ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sannan kuma tsohonministan ma’adinai.

Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi

Zaben Ekiti: Hukumar INEC ta bayar da takardan shaidar dawowa mulki ga Fayemi

Da yake karban takadar, Faayemi ya yabama hukumar INC da hukumomi tsaro yadda suka gudanar da ingantaccen aiki, inda ya bayyana cewa a yanzu ya fara shugabanci.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wata Amarya zuwa Nijar daga Katsina

Dan takarar na APC ya samu kuri’u 197,459 yayinda babban abokin adawarsa Farfesa Kolapo Olusola na jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri’u 178,121.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel