Sanata Shehu ya bayyana dalilin da yasa zai bar APC da kuma jam’iyyar dake zawarcinsa

Sanata Shehu ya bayyana dalilin da yasa zai bar APC da kuma jam’iyyar dake zawarcinsa

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya jaddada cewar har yanzu yana cikin jam’iyyar APC amma yana tattaunawa da jam’iyyar PDP.

Sanatan ya bayyana cewar shi da wasu ‘ya’yan APC na fusakantar rashin adalci da wariya daga bangaren shugabancin jam’iyyar day a gabata.

Har yanzu ban fita daga APC ba amma zan iya tabbatar maku da cewar ina tattaunawa da PDP da ma APC, abinda zai saka mu barin APC rashin adalci ne da wariya da ake nuna mana a cikin jam’iyyar.

Sanata Shehu ya bayyana dalilin da yasa zai bar APC da kuma jam’iyyar dake zawarcinsa

Sanata Shehu Sani

“An mayar da mu tamkar mujiya a cikin APC a shekaru uku da suka wuce amma muna fatan sabon shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Adams Oshiomhole zai kawo canji a inda shugabancin day a gabata ya gaza,” a cewar Sanata Sani.

DUBA WANNAN: Da duminsa: ‘Yan sanda sun cafke wani dan takarar gwamnan Borno da suke nema ruwa a jallo a wurin taron Atiku

A kwanakin baya ne kafafen yada labarai suka wallafa labarin cewar Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi sun fice daga APC kafin daga baya su fito su karyata rahotannin.

An dade ana nuna yatsa tsakanin Sanatocin Kaduna da gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa’i. Dalilin da yasa Sanatocin ke yunkurin barin jam’iyyar APC bisa zargin ba za a yi masu adalci ba a zabukan fitar da ‘yan takara na cikin gida ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel