Hukumar Hisbah ta yi ram da Almajirai 500 dake yawon bara a garin Kano

Hukumar Hisbah ta yi ram da Almajirai 500 dake yawon bara a garin Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta sanar da cafke Almajirai da mabarata daidai har da dari biyar da takwas, 508, tun daga watan Janairu zuwa watan Yunin da ta gabata, sakamakon yi ma dokar hana barace barace a birnin Kano karan tsaye.

Wani jami’in hukumar da hakkin tabbatar da dokar hana bara a Kano ya rataya akansa, Dahiru Nuhu ne ya sanar da haka a ranar Laraba,18 ga watan Yuli, inda yace daga cikin wadanda aka kama, dari biyu da talatin da takwas kananan yara ne, yayin da dari biyu da saba’in kuma manya ne.

KU KARANTA: Mugun gani: Wani Uba ya kama Ɗansa turmi da taɓarya yana luwaɗi da karamin yaro a Kaduna

Hukumar Hisbah ta yi ram da Almajirai 500 dake yawon bara a garin Kano

Mabarata

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malam Nuhu yana cewa sun kama mutanen ne a titin Dan Agundi, Hotoro, titin Lodge road, kantin kwari, titin Katsina da kuma Wapa Fagge, bugu da kari bincike ya nuna guda dari da talatim daga cikinsu yan jihar Kano, inji shi.

Haka zalika daga cikin mabaratan da aka kama, binciken hukumar ya gano akwai mutum dari uku da sittin da shida da suka fito daga jihohin Borno, Kaduna, Jigawa, Katsina da Neja, sai kuma guda goma sha biyar da suka fito daga kasar Chadi.

Malam Nuhu yace hukumar ta yi ma mabaratan adalci, inda ta saki wadanda ba’a taba kamawa da laifin ba, ma’ana wannan ne karo na farko da suka fara karya dokar, haka zalika ta saki wadanda aka gano suna da tabin hankali daga cikinsu.

Daga karshe ya shawarci jama’a da su kauce ma bara, su rungumi sana’o’I halastattu don inganta rayuwarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel