Mutuncin Najeriya ya fara dawowa: An bayyana sabon kamfanin jirgin saman Najeriya

Mutuncin Najeriya ya fara dawowa: An bayyana sabon kamfanin jirgin saman Najeriya

- Najeriya ta samu jirgin saman kanta

- A shekarun baya, Najeriya na da kamfanin jirgin sama amma an kasheta

- An kaddamar da suna, take, da tambari kamfanin a yau

Kamar yadda akayi alkawari za’a bayyana suna da kalan sabon kamfanin jirgin saman Najeriya, ministan sufurin jirgin saman Najeriya, Hadi Sirika, tare da wasu jami’an maaikatar sun bayyana sabon kamfanin jirgin saman Najeriya a yau Laraba, 18 ga watan Yuli, 2018 a Farnborough Airshow, kasar Ingila.

Yayinda yake jawabi a wajen taron kaddamarwa, Sanata Hadi Sirika ya bayyana yadda aka ayar da hannun agogon Najeriya baya a bangaren sufurin jirgin sama a shekarun baya. Ya ce Najeriya ta kasance cikin manyan masu ruwa da tsaki a bangaren amma abubuwa sun baci.

KU KARANTA: Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida

Yace: “Abin takaici, Najeriya ta kasance babbar mai ruwa da tsaki a bangaren sufurin jirgin sama na shekarun baya ta kamfanin ‘Nigeria Airways’, amma yanzu abubuwan sun bai”

“Wannan sabuwar kamfanin masu sanya hannun jari ne zasu dinga gudanar da ita. Kasuwanci ne ban a banza ba. Gwamnati ba zata sa baki wajen gudanar da ita ko wanda zai gudanar da ita na. masu sanya hannun jari ne suke da nauyin haka.”

Mutuncin Najeriya ya fara dawowa: An bayyana sabon kamfanin jirgin saman Najeriya

Mutuncin Najeriya ya fara dawowa: An bayyana sabon kamfanin jirgin saman Najeriya

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafan yada labarai, Bashir Ahmed, ya tofa albarkacin bakinsa kan wannan cigaba, yace: “Abinda suka kashe shekaru da yawa, shugaba Muhammadu Buhari na rayawa.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel