Yanzu-yanzu: An damke yan Boko Haram 8 da sukayi garkuwa da yan matan Chibok

Yanzu-yanzu: An damke yan Boko Haram 8 da sukayi garkuwa da yan matan Chibok

Yan Boko Haram takwas da ake zargin sun yi musharaka wajwn garkuwa da yan matan makarantan sakandaren Chibok 276 sun shiga hannun hukumar yan sanda a garin Maiduguri, birnin jihar Borno.

Yan Boko Haram takwas din na cikin yan ta’adda 22 da sashen leken asirin hukumar yan sandan Najeriya ta damke a jihar Borno, Adamawa, da sauran jihohi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Daga cikin sauran akwai wadanda suka bada gudunmuwa wajen hare-haren kunar bakin wake 50 a jihar Borno da Adamawa.

Yanzu-yanzu: An damke yan Boko Haram 8 da sukayi garkuwa da yan matan Chibok

Yanzu-yanzu: An damke yan Boko Haram 8 da sukayi garkuwa da yan matan Chibok

Kana sun kai wasu hare-hare da yayi sanadiyar mutuwan dubunnan yan Najeriya.

An yi garkuwa da dalibai mata a makarantan GGSS Chiboka a ranan 14 ga watan Afrilu, 2014. Wannan abu ya tayar da hankalin duniya a shekarun baya.

KU KARANTA: Zahra Buhari da mijinta Ahmed Indimi sun radawa yaronsu suna “Muhammad”

Zuwa yanzu, mata 112 ne kawai aka samu daman cetowa sanadiyar sulhu da cinikayya da akayi tsakanin gwamnatin tarayya da yan Boko Haram.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel