Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Sakkwato, Alhaji Isa Sadiq Achida, yace babu wata dalili da zai sanya jam'iyyar ta bawa gwamna Aminu Waziri Tambuwal 'jan kati' saboda bai aikata wata laifi da zai sa a kore shi ba.

Achida ya fadi hakan ne yayin da yake tsokaci kan ikirarin da gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi inda yace jam'iyyar ta APC ta kore shi daga filin wasa ta hanyar bashi 'jan kati', inda Achida yace gwamnan kawai yana neman dalilin tafiya wata jam'iyyar ne.

Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

Babu dalilin bawa gwamna Tambuwal 'jan kati' - APC

DUBA WANNAN: Yadda daga addu'a wani dan tsibu ya zake wa wata daliba

Akwai jita-jita dake zagawa inda ake cewa bayan gwamna Samuel Ortom din, wasu daga cikin gwamnonin APC ciki har da Tambuwal na shirin ficewa daga jam'iyyar ta APC.

Sai dai Achida yace bashi da masanaiya a kan wannan batun a jihar Sakwato. "Muna tare da gwamna Aminu Tambuwa 100% kuma a iya sani na komi na tafiya lami lafiya," inji shi.

"Muna tare da gwamna Tambuwal. Babu wata laifi da ya aikata ko saba doka da yayi, yana tare da APC 100%, yana bamu goyon baya kuma yana biya mana duk bukatun mu a jihar."

A kan jita-jitar cewa Tambuwal zai fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP, Achida yace shi wannan shine karo na farko da ya fara jin batun a bakin yan jarida.

"Ban taba jin labarin ba; bai fada mana komai mai kama da wannan ba kuma bani da masaniya akan batun," inji shugaban jam'iyyar reshen jihar Sakkwato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel