Jami'an tsaro sun kama mutane 7 akan kashe-kashen Plateau

Jami'an tsaro sun kama mutane 7 akan kashe-kashen Plateau

Jami’an tsaro na Operation Safe Haven (OPSH) sun sake kama wasu Karin mutane guda bakwai dake da hannu a kashe-kashen jihar wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Yuni a Barkin Ladi da karamar hukumar Riyom na jihar Plateau.

Mukaddashin daraktan labarai na hukumar tsaro, Birgediya Janar John Agie, wanda ya gurfanar da masu laifin a jiya a hedkwatar rundunar dake Jos, yace “Na zo daga Abuja a yaudomin ci gaba da tattara bayanai akan bincikenmu na abun da ya faru a watan da ya gabata.

“Dakarun mu suna bibiyar masu laifin da suka kai hare-hare a ranar 23 ga watan Yuni har yanzu, sannan hakan yayi sanadiyan kama mutane biyu – Ibrahim Choji da Ahmadu Ibrahim. Wadannan biyun na daga cikin mutanen da suka kai hari kauyen Zongo a ranar 23 ga watan Yuni.

Jami'an tsaro sun kama mutane 7 akan kashe-kashen Plateau

Jami'an tsaro sun kama mutane 7 akan kashe-kashen Plateau

"Muna da wasu mutane uku a hannu - Shuaibu Suleman, Buhari Shuaibu, Zakamin Abdulkadri – daga cikin wadanda suka kai hari kauyen Josho dake yankin Bokkos a ranar 14 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Ina kwace babura ne saboda mutane sun daina gina gidaje – Mai aikin gini

“Bayan wannan gurfanarwan, za mu mika su gay an sanda domin ci gaba da bincike sannan daga nan za’a hukunta su."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel