2019: Duk wani taron dangi ba zai yi tasiri akan Buhari ba - Goni

2019: Duk wani taron dangi ba zai yi tasiri akan Buhari ba - Goni

Shugabar kungiyar masoyan Buhari wato Grassroots Mobilizers for Buhari (GMB), na Ambassador Fatima M. Goni, ta yi Allah wadai da abun da ta bayyana a matsayin makircin yan siyasa na hada kai domin karkatar da hankali mutane daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ta bayyana cewa wannan makirci na jam’iyyar PDP da ta hade da jam’iyyun siyasa domin ta muzgunwa shugaba Buhari ba zai yi tasiri ba.

A cewarta, wannan kungiyar gammaya da ta hade ba ta da wani ajiyayyen ajanda na kawo ci gaba a kasar da yan Najeriya.

Ta bayyana cewa kamata yayi wannan jam’iyyar ta mayar da hankali wajen ba yan Najeriya hakurin muzguna masu da jam’iyyar PDP ta yi a shekaru goma sha shida da ta kwashe tana mulki.

2019: Duk wani taron dangi ba zai yi tasiri akan Buhari ba - Goni

2019: Duk wani taron dangi ba zai yi tasiri akan Buhari ba - Goni

Ta bukaci yan kungiyar R-APC da kada su yi kuskuren da PDP zata yi amfani das u wajen cimma manufarta sannan ta yasar da su.

KU KARANTA KUMA: Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi

Ta ce su tuna da cewar Shugaba Buhari dan damokradiyya ne mai sauraron kukan mutane a koda yaushe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel