Ina kwace babura ne saboda mutane sun daina gina gidaje – Mai aikin gini

Ina kwace babura ne saboda mutane sun daina gina gidaje – Mai aikin gini

Yan sandan jihar Niger sun kama wasu barayin Babura guda biyu da suka addabi unguwaar Kpakungu dake karamar hukumar Chanchaga na jihar.

Jami’an yan sanda ne suka kama masu laifin, Danjuma Idris, 28, da Mohammed Kudu, 27 bayan sun yiwa wani Johnson Emeka dake Ketaren Gwari fashin babur dinsa kirar Jingcheng.

Northern City ta tattaro cewa a ranar Talata wani Abdulsalami Abdulkareem, 27 ya kama yan fashin a Farm Centre Tunga, domin kai babur din ga wani Sadam Dutse a jihar Kaduna.

Bincike ya nuna cewa masu laifin sun dauki tsawon lshekaru da dama suna wannan aikin na fashi kafin a kama su.

Ina kwace Babura ne saboda mutane sun daina gina gidaje – Mai aikin gini

Ina kwace Babura ne saboda mutane sun daina gina gidaje – Mai aikin gini

Daya daga cikin masu laifin Idris ya fadama majiyarmu cewa an dauko su ne domin mika babur ga Dutse a Kaduna don ya samu yan kudi da zai tafiyar da lamuransa nay au da kullun.

KU KARANTA KUMA: Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi

Ya bayyana cewa ya shiga wannan harka ne tsawon lokaci saboda mutane sun daina gine-gine don haka baya samun kudi a matsayinsa na mai aiki gine-gine.

Ya kuma daura laifin akan gwamnatin tarayya na rashin basu aikin yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel