Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi

Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da sarkin garin Jakura dake karamar hukumar Lokoja na jihar Kogi, Cif Usman Ajibola sannan kuma suka kashe dansa Rufai Ajibola.

Kakakin yan sandan jihar Kogi, Mista William Ayah ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels Television a ranar Talata, 17 ga watan Yuli.

Basaraken da dansa na a hanyarsu ta dawowa daga garin Oworo lokacin da masu garkuwan suka kai masu hari a tsakanin al’umman Imo da Igbonla kimanin kilomita 15 da garin Jakura.

Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi

Anyi garkuwa da Basarake sannan aka kashe dansa a Kogi
Source: Depositphotos

Masu garkuwan kimanin su biyar sun dauke basaraken tare da direbansa sannan suka kashe masa dansa yayinda yake kokarin ceto mahaifin nasa.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Makiyaya: An kashe sama da mutum 500 a Filato, Nasarawa, Kogi, da Benuwai

Yan sandan sun bayyana cewa suna bincikar lamarin a yanzu haka.

A halin da ake ciki, an dauki gawar marigayi Rufai zuwa dakin ajiye gawa a Lokoja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel