‘Yan takaran da za su gwabza da Gwamna El-Rufai a zaben 2019

‘Yan takaran da za su gwabza da Gwamna El-Rufai a zaben 2019

Yayin da ake shirin buga gangar 2019, mun kawo maku wasu manyan ‘Yan siyasan da ake tunani za su buga da Gwamna Nasir El-Rufai wanda yake kan karagar mulki a halin yanzu.

Isa Ashiru wanda ya wakilci Kudan da Makarfi yana neman kujerar El-Rufai

Ana kishin-kishin din cewa Sanata Shehu Sani ya janye takarar sa, amma har yanzu akwai wadanda za su yi takara a 2019 da El-Rufai. Watakila daga ciki akwai:

1. Mukhtar Ramalan Yero

Ana kokarin zuga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa. Ramalan Yero ya sha kashi ne a hannun Nasir El-Rufai na Jam’iyyar APC a zaben 2015. Alhaji Yero yana da Magoya musamman a Zaria.

2. Isa Muhammad Ashiru

Isa Ashiru Kudan na cikin wadanda za su iya gwabzawa da Gwamna El-Rufai. Tsohon ‘Dan Majalisa wanda yayi takarar Gwamna a 2015 a APC kila nemi kujera wannan karon a Jam’iyyar adawa na PDP. Kudan rikakken 'Dan siyasa ne mai jama'a.

3. Dr. Muhammad Sani Bello

Sani Bello wanda shi ne Mainan Zazzau yana cikin masu harin kujerar a karkashin Jam’iyyar PDP. Bello rikakken ‘Dan Boko ne masanin harkar kudi yana aiki ne da Kungiyar ECOWAS. Bello tsohon Kwamishinan Jihar ne kuma ya dade yana siyasa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel