Shehu Sani ya fasa takaran kujeran gwamnan jihar Kaduna?

Shehu Sani ya fasa takaran kujeran gwamnan jihar Kaduna?

Labarai daga majiya mai karfi na nuna cewa dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Kwamred Shehu Sani, yaajiye niyya takaran kujeran gwamnan jihar Kaduna yayinda yake kokarin samu tikitin sake takaran kujeran majalisa.

Majiya a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyanawa jaridar Leadership cewa Sanatan na cikin tattaunawa da PDP domin samun tikitinsu na takara kujerar majalisa, inda an cimma matsaya, zai bar jam’iyyar APC.

Wannan sannanan dan siyasar PDP a jihar Kaduna wanda ke da masaniya game da wannan abu ya ce da kamar wuya Shehu Sani ya samu tikitin kujerar gwamna karkashin PDP idan yayi takara da sauran yan takaran.

Yace: “Mun tattauna a ganawar da mukeyi, nan ba da dadewa ba, za’a cimma matsaya. A matsayinmu na jam’iyya, kofofinmu na bude ga duk wanda yake son shigowa. Zai fi masa yayi sake takaran kujerar majalisa saboda lokaci ya kure masa kuma har yanzu bai canza sheka ba.”

Za ku tuna cewa sanata Shehu Sani a lokuta da dama ya jaddada cewa zai yi takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2019.

Wani jigon jam’iyyar APC, Tanko Wusono, ya ce Shehu Sani ba zai iya samun tikitin takarar gwamna ba da na dan majalisa a jam’iyyar APC saboda rikicinsa da gwamnan jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel