Boko Haram na sake dandazo a Jihar Borno - Hukumar Soji

Boko Haram na sake dandazo a Jihar Borno - Hukumar Soji

Kwamandan gudanarwar Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya bayyana cewa, wasu mambobin kungiyar ta'adda ta Boko Haram na sake dandazo domin karfafa kungiyar su a yankunan karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Manjo Nicholas ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri, inda yace wasu 'yan ta'adda sun kai hari kan dakarun sojin dake kauyen Bama a ranar Asabar din da ta gabata.

Yake cewa, 'yan ta'adda sun kai aiwatar da harin ne yayin da dakarun ke gudanar da sintiri a yankin karamar hukumar ta Bama.

Boko Haram na sake dandazo a birnin Maiduguri

Boko Haram na sake dandazo a birnin Maiduguri

Kamar yadda kwamandan sojin ya bayyana, 'yan ta'addan sun samu damar gudanar da wannan hari ne a sanadiyar makalewa da motocin dakarun suka yi cikin yunbu da tabo sakamakon yanayi na kasancewar hanyar cikin lokuta na damina.

Sai dai babban dakarun sojin ya musanta rahotonni dake yaduwa na cewar wasu dakarun sojin sun bace bayar afkuwar harin, inda ya ce ko shakka babu kamshin a wannan batutuwa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta tallafa tare da biyan diyya ga wadanda Ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Katsina - Osinbajo

Nicholas ya lura da cewar dole sai hukumar sojin kasa ta sake sabon salo da tsarin gudanarwar ta musamman a wannan lokuta na damina domin ci gaba da samun nasara da galaba kan 'yan ta'adda kamar yadda ta saba a lokutan baya.

Legit.ng ta fahimci cewa, kakakin hukumar sojin kasa Birgediya Janar Texas Chukwa, ya karyata rahoton bacewar dakarun soji 23 bayan farmakin da 'yan ta'addan suka kai a karshen makon da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel