Mataimakin gwamnan wannan jihar ya roki kotu ta hana a tsige shi

Mataimakin gwamnan wannan jihar ya roki kotu ta hana a tsige shi

Yayin da ake cigaba da takaddama a tsakanin mataimakin gwamnan jihar Imo, Prince Eze Madumere dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya da kuma majalisar dokokin jihar kan shirin su na tsige shi, yanzu haka ya ruga kotu yana rokon ta hana a yi masa wannan danyen aikin.

Wannan kau na zuwa ne kamar yadda muka samu duk da daruruwan magoya bayan mataimakin gwamnan sun fito a saman tituna a jihar suna zanga-zangar shirin na tsige gwamnan na su.

Mataimakin gwamnan wannan jihar ya roki kotu ta hana a tsige shi

Mataimakin gwamnan wannan jihar ya roki kotu ta hana a tsige shi

KU KARANTA: Gwamnoni 5 a Arewa da ake tunanin ba za su zarce ba

Legit.ng ta samu cewa kakakin majalisar ne dai Acho Ahim da wasu 'yan majalisar 13 ne suka sanyawa takardar soma tsige mataimakin gwamnan hannu.

Sai dai binciken majiyar mu ya bankado cewa 'yan majalisar na da goyon bayan gwamnan jihar ne Rochas Okorocha wanda ya ce gwamnan na sa ya dena yi masa da'a da biyayya haka kuma ya dena halartar duk wani aikin sa.

'Yan majalisun da suke shirin tsige mataimakin gwamnan dai sune Lawrence Duruji (Ehime Mbano), Uche Ejiogu (Ihite Uboma), Henry Ezediaro (Oguta), Chika Madumere (Nkwerre), Uju Onwudiwe (Njaba), Ngozi Obiefule (Isu), Victor Onyewuchi (Owerri west), Maxwell Odunze (Orlu), Ugonna Ozuruigbo (Nwangele), Chinedu Offor (Onuimo), Ikechukwu Amuka (Ideato South ), Lloyd Chukwuemeka (Owerri North), da kuma Arthur Egwim (Ideato North).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel