Gwamna Fayose yayi watsi da barazanar Hukumar zabe INEC

Gwamna Fayose yayi watsi da barazanar Hukumar zabe INEC

Kwanakin baya ne Gwamna Ayo Fayose ya debo ruwan dafa kan sa inda ya tashi ya sanar da sakamakon zaben Gwamnan Jihar Ekiti a gidan rediyo ganin cewa PDP za ta sha kasa a zaben.

Gwamna Fayose yayi watsi da barazanar Hukumar zabe INEC

INEC da EFCC sun taso Gwamna Ayo Fayose a gaba

Sanar da sakamakon zaben bogin da Gwamna Fayose yayi ta sa aka rufe gidan rediyon na Jihar Ekiti. Doka dai ba ta kowa damar wannan aiki ba sai Hukumar zabe na kasa INEC a tsarin mulki, kuma ana iya hukunta wanda ya sabawa dokar.

Hukumar zabe na kasa watau INEC ba ta ji dadin wannan danyen aiki na Gwamna Ayo Fayose ba. Gwamnan ya sanar da cewa Jam’iyyar sa ta PDP mai mulkin Jihar a yanzu ce ta ke shirin lashe zaben wanda hakan ya zama ba gaskiya ba.

KU KARANTA: Gwamnan Ekiti ya jawowa kan sa fushin INEC

Wata babbar Kwamishinan Hukumar ta INEC watau Amina Zakari ta aikawa Gwamna Fayose takarda ta hannun wani Lauyan ta Ubong Akpan inda ta nemi ya janye kalaman sa. Kwamishinar zaben tace Ayo Fayose ya ci mata mutunci.

Kusan kwana biyu kenan da su ka wuce, Kwamishinar zaben ta nemi Gwamnan na Ekiti ya fito gaban Duniya ya nemi afuwa game da furucin na sa. Har yanzu dai Gwamnan bai fito yayi jawabi ya bada hakuri ba kuma ga wa’adin ya kawo.

Kwanaki sai dai ma aka ji Gwamnan yana cewa murde zaben sabon Gwamnan Ekitin da aka yi. Gwamnan ya kuma ce ba zai taya Kayode Fayemi na APC murnar lashe zaben da yayi ba. Ba mamaki dai yanzu INEC ta shigar da kara Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel