Bacewar sojoji: Wasu 'yan Arewa sun yi wa Atiku Abubakar wankin babban bargo

Bacewar sojoji: Wasu 'yan Arewa sun yi wa Atiku Abubakar wankin babban bargo

Wata kungiyar mazauna yankin Arewa ta tsakiya da aka fi sani da 'Middle Belt' a turance sun yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar zama shugaban kasa a 2019, Alhaji Atiku Abubakar suka kakkausa game da kamalan sa akan sojojin Najeriya da aka ce sun bace.

Kungiyar mai suna, Middle Belt Conscience Guard (MBCG) ta ce kalaman na tsohon shugaban kasar abun takaici ne kuma hakan yana nuna cewa shi ba mai son kasa bane da cigaban ta.

Bacewar sojoji: Wasu 'yan Arewa sun yi wa Atiku Abubakar wankin babban bargo

Bacewar sojoji: Wasu 'yan Arewa sun yi wa Atiku Abubakar wankin babban bargo

KU KARANTA: Majalisar dattijai ta amince da sabbin nade-nade 7 daga Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa tun farko Atiku Abubakar ya ce ya damu matuka game da halin da sojojin Najeriya da suka bace har su 23 a kauyen Boboshe na karamar hukumar Bama a satin da ya gaba.

Sai dai kungiyar ta Middle Belt Conscience Guard (MBCG) ta ce kamata yayi Atiku din yayi bincike game da lamarin ba wai kawai ya rika magana ba domin kawai wata manufa na sa ta siyasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel