Daga karshe, Saraki yayi karin haske game da barin sa jam'iyyar APC

Daga karshe, Saraki yayi karin haske game da barin sa jam'iyyar APC

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Bukola Saraki a ranar Talatar da ta gabata da za'a iya cewa shine karo na farko da yin magana a game da rade-raden komawar sa APC ya bayyana cewa zai fitar da sahihiyar sanarwa idan har hakar ta tabbata.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta kamfanin dillacin labaru, Saraki ya yi wannan kalamin ne a filin sauka da tashin jirage a garin Ilorin na jihar Kwara lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Daga karshe, Saraki yayi karin haske game da barin sa jam'iyyar APC

Daga karshe, Saraki yayi karin haske game da barin sa jam'iyyar APC

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya suna alhinin rabuwa da Fayose

Legit.ng ta samu cewa haka zalika da aka tambayi Saraki din game da tsokacin sa akan nasarar da ya samu a kotun koli kan zargin da ake yi masa na yin karya wajen bayyana kadarorin sa, Saraki yace daman yana da yakinin cewa gaskiya zata yi halin ta.

Daga nan ne kuma sai Saraki din tare da dumbin magoya bayan sa suka dunguma zuwa fadar Sarkin garin Alh Ibrahim Sulu- Gambari domin gaisuwa da zumunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel