Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida

Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida

A ranar Talatar da ta gabata ne dai muka samu cewa babbar kotun jihar Filato dake zamanta a garin Jos ta dage shari'ar da take yi a tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan jihar Sanata Jonah Jang kan wasu zarge-zargen sama da fadi da dukiyar al'ummar jihar.

Mun samu cewa alkalin da ke shari'ar a kotun mai suna Mai Shari'a Damiel Longji ne ya dage karar har sai zuwa watan Oktaba mai kamawa kamar yadda hukumar ta EFCC ta bukata domin samun damar gabatar da shedun ta.

Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida

Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida

KU KARANTA: Kashe-kashe; Babban malamin addini ya yi kaca-kaca da Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa tun farko EFCC din ta roki kotun ta dage cigaba da shari'ar ne saboda a cewar ta shedun ta sun ce ba za su iya gurfana a gaban kotun ba saboda dalilan tsaro na jihar.

Sai dai alkali mai shari'a a kotun yayi barazanar soke karar idan har hukumar ta EFCC ta cigaba da yin tafiyar hawainiya akan shari'ar.

Su ma dai tawagar lauyoyin da ke kare tsohon gwamnan sun bayyana cewa abun takaici ne hujjar da hukumar ta EFCC din ta bayar domin kuwa bai kamata ma ace ta fito daga bakin ta ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel