Majalisar dattijai ta tabbatar da wasu sabbin nade-nade 7 da shugaba Buhari yayi

Majalisar dattijai ta tabbatar da wasu sabbin nade-nade 7 da shugaba Buhari yayi

Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talatar da ta gabata ta tabbatar da nadin tsohon Sifeton Janar na 'yan sandan Najeriya Musiliu Adeola Smith a matsayin shugaban hukumar gudanarwar harkokin 'yan sandan Najeriya watau Police Service Commission (PSC), kamar yadda shugaba Buhari ya bukata.

Sauran wadanda majalisar ta amince da su sun hada da kwamishinonin din-din-din a hukumar su biyu da suka hada da Clara Bata Ogunbiyi daga Arewa maso gabas da kuma Lawal Bawa daga Arewa maso yamma.

Majalisar dattijai ta tabbatar da wasu sabbin nade-nade 7 da shugaba Buhari yayi

Majalisar dattijai ta tabbatar da wasu sabbin nade-nade 7 da shugaba Buhari yayi

KU KARANTA: 2019: An hana Dankwambo kafa allunan kamfe din sa a jihar Adamawa

Legit.ng ta samu cewa haka zalika majalisar dattijan ta amince da nadin mambobin hukumar da suka hada da Muhammad Naja’atu daga Arewa ta yamma; Braimoh Adogame Austin daga kudu maso kudancin Najeriya; Rommy Mom daga yankin Arewa ta tsakiya da kuma Dakta Nkemka Oshimiri Jombo-Ofo daga kudu maso gabashin kasar.

A wani labarin kuma, 'Yan majalisar jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya sun aike da takardar shirin su na soma tsige mataimakin gwamnan jihar Prince Eze Madumere zuwa gare shi a hukumance.

Wannan kau na zuwa ne kamar yadda muka samu duk da daruruwan magoya bayan mataimakin gwamnan sun fito a saman tituna a jihar suna zanga-zangar shirin na tsige gwamnan na su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel