Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake a Lokoja, sun bindige Dansa

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake a Lokoja, sun bindige Dansa

Wani hakimi a garin Jakura dake cikin karamar hukumar Lokoja na jihar Kogi, Usman Ajibola ya fada hannun wasu miyagu masu garkuwa da mutane bayan wani hari da suka kai masa, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, William Ayah ne ya tabbatar da haka a ranar Talata,17 ga watan Yuli, inda ya bayyana a yayin harin da yan bindigar suka kai, sun bindige yaron Basarake Usman.

KU KARANTA: Kaico! Wani Matashi ya daddatsa Mahaifiyarsa gunduwa gunduwa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito masu garkuwan suna far ma Basaraken tare da yaronsa ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga garin Oworo zuwa Jakura, inda suka yi awon gaba da Basarake da Direbansa, sa’annan suka kashe Dansa a lokacin da yayi yunkurin kwato mahaifinnasa.

Sai da Kaakaki Williams yace tuni rundunar Yansandan jihar ta fara gudanar da binciken kwakwaf game da lamarin, sa’annan an mika gawar mamacin, Rufai Ajibola zuwa dakin ajiyan gawarwaki dake garin Lokoja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel