Yadda Kididdigar kasafin kudin zaben 2019 za ta kasance - Buhari

Yadda Kididdigar kasafin kudin zaben 2019 za ta kasance - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake gabatar da wani sabon tsari cikin kasafin kudi ga majalisar dokoki ta tarayya domin neman sahalewar ta kan Naira Biliyan 167 cikin Naira biliyan 242 na adadin kudi da zaben 2019 zai lashe.

Jagoran kasar ta Najeriya dai ya bayyana cewa, hukumar zabe ta kasa watau INEC da sauran hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki kan harkokin gudanar zabe, za su bukaci Naira Biliyan 242 domin gudanar da zaben na badi cikin aminci.

A sanadiyar haka ne shugaba Buhari ya nemi majalisar ta kasa kan tanadin Naira biliyan 164 cikin kasafin kudin 2018, inda kasafin kudin 2019 zai tanadi ragowar kudaden na kimanin Naira biliyan 78 domin gudanar da babban zabe a shekarar ta badi.

Zaben 2019 zai lashe N242bn - Shugaba Buhari ya shaidawa Majalisar Tarayya

Zaben 2019 zai lashe N242bn - Shugaba Buhari ya shaidawa Majalisar Tarayya

Buhari cikin wata rubutacciyar wasika da ya aikawa majalisar ta tarayya, ya nemi mambobin ta akan su ware wani kaso cikin adadin kudi na Naira biliyan 578 da aka kasafta cikin kasafin kudin 2018 domin gudanar da manyan ayyuka musamman na gine-gine domin tanadi ga babban zabe.

Bugu da kari shugaba Buhari ya gargadi majalisar kan kada ta kuskura ta tumfaya adadin kasafin kudin 2018 daga matsayar sa ta Naira tiriliyan 9.21, sai dai ya nemi ta yaso wani kaso daga cikin kasafin kudin manyan ayyuka da aka riga da kasaftawa.

KARANTA KUMA: Cikin ƙanƙanin lokaci zan kawo ƙarshen Boko Haram a Najeriya - Atiku

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, shine ya gabatar da abinda wasikar shugaban kasa ta kunsa yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

Kazalika Legit.ng ta kawo muku kididdigar wannan kasafin kudi na zaben 2019 da shugaba Buhari ke neman sahalewar majalisar da kuma tanadi wannan adadin kudi da za a batar yayin zaben kamar haka:

Hukuma zabe ta kasa watau INEC: N189.2bn

Hukumar bayar da shawara kan harkokin tsaro ta kasa: N4.2bn

Hukumar DSS: N12bn

Hukumar Civil Defence: N3.5bn

Hukumar 'yan sanda: 30.5bn

Hukumar shige da fice: 2bn

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel