Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyarar jaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyarar jaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Katsina don jajanta ma mutanen da ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane ashirin, tare da asarar dimbin miliyoyi.

Osinbajo ya isa jihar Katsina da tsakar rana inda ya samu tarba daga gwamnan jihar, Aminu Belo Masari, bayan ya halarci bikin bude sabon kamfanin Siminti na BUA a garin Kalambaina na jihar Sakkwato.

KU KARANTA: Kaico! Wani Matashi ya daddatsa Mahaifiyarsa gunduwa gunduwa

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyarar jaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Mataimakin shugaban kasa

Saukarsa filin jirgi na tunawa da Umaru Musa Yar’adua ke da wuya, sai ya garzaya karamar hukumar Jibia, garin da ibtila’in ya fi shafa, kuma ya bayyana musu alhininsa da na shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa:

“Shugaba Buhari ya umarceni na tabbatar da cewa zamu dukkanin mai yiwuwa don ganin mun kula da duk wadanda lamarin ya shafa, haka zalika yace na tabbatar muku ba zamu sake bari wannan lamari ya maimaitu ba.

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyarar jaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Mataimakin shugaban kasa

“Muna da yancin rayuwa a matsayinmu nay an Najeriya, kuma muna da yancin a kula da mu, bugu da kari gwamnatin tarayya ta hada kai da gwamnatin jihar Katsina don ganin mun saukaka muku radadin da kuke fama da ita a yanzu.” Inji Osinbajo.

Daga karshe Osinbajo yace: “Zamu biya kudin fansa a inda ya kamata a biya fansa, kuma zamu sake yin gini, a inda ake bukatar gini.”

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyarar jaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu rakiyar Ministan tama da karafa, Alhaji Abubakar Bawa Bwari tare da shugaban hukumar bada agajin gaggawa, Mustapha Maihaja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel