Abin Azimun ne: Shugaba Buhari ya nemi taimakon kotun tuhumar aiyukan ta’addanci ta duniya (ICC) a kan yaki da cin hanci

Abin Azimun ne: Shugaba Buhari ya nemi taimakon kotun tuhumar aiyukan ta’addanci ta duniya (ICC) a kan yaki da cin hanci

- Shugaba Buhari ya yi kira a fadada hurumin kotun ICC domin tuhumar manyan laifukan yaki da cin hanci a duniya

- Da yake jawabi yau a birinin Hague na kasar Holland, shugaba Buhari ya yiwa duniya alkawarin gabatar da zabe mai tsafta a shekarar 2019

- Shugaba Buhari ya bayyana cewar, tabbas ICC na da rawar takawa a bangaren ganin cewar duk wadanda suka sace dukiyar kasashensu an hukunta su

Shugaba Buhari ya yi kira ga kasashen dake zaman mambobi a kotun tuhumar aiyukan ta’addanci na duniya(ICC) da su amince a fadada hurumin kotun domin tuhumar manyan laifukan yaki da cin hanci a kasashensu.

Da yake jawabi yau a birinin Hague na kasar Holland, shugaba Buhari ya yiwa duniya alkawarin gabatar da zabe mai tsafta a shekarar 2019 sabanin irin wanda aka yi a shekarar 2011 da har saida kotun ta kafa kwamitin bincike.

Abin Azimun ne: Shugaba Buhari ya nemi taimakon kotun tuhumar aiyukan ta’addanci ta duniya (ICC) a kan yaki da cin hanci

Shugaba Buhari a ICC

Kotun ICC na iya bayar da gudunmawa wajen dakile cin hanci a kasashen dake fama da matsalar satar dukiyar gwamnati ta hanyar gurfanar da duk wanda ya wawuri dukiyar al’umma tare da hukunta shi ba tare da wani bata lokaci,” a cewar shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta koma haushin kare bayan dawowa daga wurin wani malamin tsibbu

Shugaba Buhari ya bayyana cewar, tabbas ICC na da rawar takawa a bangaren ganin cewar duk wadanda suka sace dukiyar kasashensu, suka hana kasarsu samun cigaba, sun gurfana gabanta tare da yi masu hukunci da zai zama darasi ga masu rike da amanar dukiyar al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel