Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

- Sa toka sa katsin PDP da tsohon shugaban jam'iyyar ya bar baya da kura

- Kotu ta ci tarar jam'iyyar zunzurutun kudi har Naira N600,000

Jam’iyyar PDP a yau Talata ta yi rashin nasarar kalubalantar korafin hukuncin wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas, wanda ya tabbatar da tsagen Adebayo Dayo a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ta PDP a jihar Ogun.

Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

Jaridar The Punch ta rawaito cewa reshen babbar kotun daukaka karar ne dake jihar Legas ya kori rokon da PDP ta shigar, sannan ta kuma umarce ta da ta biya N600,000 a matsayin tara ga tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Ali Modu-Sheriff da Farfesa Wale Oladapo da kuma Adebayo Dayo.

Bayannan da ke risker Legit.ng sun nuna cewa tun farko babbar kotun tarayyar ce ta baiwa uwar jam’iyyar PDP ta kasa umarnin karbar tsagin Dayo a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na jihar ta Ogun, kuma wa’adinsa zai kare ne a shekarar 2020.

A bisa rashin amincewa da hukunci ne ya sanya PDP ta tafi zuwa babbar kotun daukaka kara, amma sai dai jam’iyyar ta hannun daya daga cikin lauyoyinta mai suna Godwill Mrakpor daga baya ta sauya shawara ta janye, hakan ta sanya kotun ta soke karar.

KU KARANTA: Rana zafi inuwa kuna: Gwamnati ta yi ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose daurin talala

Amma kuma wane tudu wane gangare sai gashi wani lauyan PDP mai suna Dr Yemi Oke ya sake komawa dauke da wani kunshin korafin kan maganar, yana ikirarin cewa tsagin tsohon shugaban jam’iyyar Ali Modu-Sheriff ne ya kyankyasawa lauya Mrakpor don ya dakata da daukaka karar ba gaskiya ba ne.

Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu

Rashin nasarar PDP a kotu ya jawo zata biya N600,000 ga Ali Modu-Sheriff da wasu mutune biyu
Source: Facebook

Sai dai kuma kotun daukaka karar a ranar 11 ga watan Yuli a wata shari’a da alkali Jamilu Tukur ta tabbatar da cewa Modu-Sheriff din na da damar dakatar da karar kamar yadda su kayi.

Mai shari’ar ya ce “Daga kowanne bangare na kalli bukatar, yafi rinjaye da yiwuwar iya janyewa”.

"A don haka bayan duba na tsanaki, bisa yadda abubuwan suka kasance da kuma gaza bin umarnin hukuncin da wannan kotun ta yanke, don haka PDP zata biya tarar N200,000 ga mutane ukun da ke cikin shari’ar (Dayo, Modu-Sheriff and Oladapo).”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel