‘Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a jihar Zamfara

‘Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a jihar Zamfara

- Bayan kai harin 'yan bindiga garin Malikawa dake yankin Gidan Gona, sun sake yunkurin kai wani harin

- Amma sai dai jami'an 'yan sanda cikin bajinta da jajircewa suka dakile yunkurin nasu

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta bayyana nasarar da ta yi wajen dakile wani hari da yan bindiga su kayi yunkurin kaiwa garin Tangaram dake karamar hukumar Anka a jihar.

‘Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a jihar Zamfara

‘Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a jihar Zamfara

Hakan ya fito ne daga wani jawabi dake dauke da sa hannun kakakin hukumar, Muhammad Shehu a yau Talata.

Kakakin ya bayyana a cikin jawabin cewa hukumar ta hada jami'ai inda suka garzaya yankin domin kaiwa jama'a dauki.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari kauyen jihar Zamfara

Kuma sun dauki tsawon lokaci suna artabun musayar harbi wanda daga bisani suka yi nasarar harbe daya daga ciki har lahira, sauran yan bindigar kuma sun tsere dauke da raunuka daban-daban. A cewar kakakin

A cikin jawabin dai an bayyana cewa, "A ranar asabar ne 14 ga wata muka samu rahoton ‘yan bindiga sun shiga yankin Tangaram domin kai hari, amma hakarsu bata cimma ruwa ba".

"Hukumar mu ta shirya jami'ai wanda suka dauki lokaci suna artabu da yan bindigar, a karshe dai an yi nasarar harbe guda daga ciki yayin da sauran suka arce cikin raunukan harbin bindiga".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel