Cikin ƙanƙanin lokaci zan kawo ƙarshen Boko Haram a Najeriya - Atiku

Cikin ƙanƙanin lokaci zan kawo ƙarshen Boko Haram a Najeriya - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin kawo karshen ta'addancin Boko Haram a kasar nan muddin aka kada masa kuri'u da za su tabbatar da nasarar sa a zaben kujerar shugaban kasa na 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasar dake fafutikar nema tikitin takara na jam'iyyar sa ta PDP ya bayyana cewa, cikin ƙanƙanin lokaci gwamnatin sa za ta kawo karshen ta'addancin Boko Haram da yaƙi ci yaƙi cinyewa a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan tun shekaru 9 da suka gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta bayyana, Atiku ya bayyana hakan ne ga magoya bayan jam'iyyar PDP a dakin tarin na Forshams dake birnin Maiduguri a jihar Borno yayin yawon zagaye na wasu sassan kasar nan domin gudanar da yakin neman zabe.

Cikin ƙanƙanin lokaci zan kawo ƙarshen Boko Haram a Najeriya - Atiku

Cikin ƙanƙanin lokaci zan kawo ƙarshen Boko Haram a Najeriya - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, an kawo karshen yakin basasa cikin lokacin da bai wuci shekaru biyu da rabi ba sai dai tsawon shekaru 9 da suka gabata yaki da Boko Haram ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Jerin 'yan wasa 5 na Duniya mafi daukar albashi a shekarar 2018

Yake cewa, "Najeriya ta ga bayan yaƙin basasa cikin shekaru biyu da rabi duk da kasancewar ƙungurmin daji dake yankin Kudu maso Gabashin kasar nan. Ina mamakin yadda yaƙi da Boko Haram ya dauki har tsawon shekaru 9. Dole akwai tangarda dake labe a wani wuri na daban."

"Muddin aka zabe ni ba zan yi dakon sauraron wani kwamandan Soji ba. Dole mu kawo karshen ta'addancin cikin mafi ƙanƙanin lokaci domin kuwa ya tagayya duk wata gudanarwa a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel